Labarai
An cigaba da sauraron shari’ar Yunusa Yellow
A yau Talata kotun ɗaukaka ƙara da ke birnin Rivers a jihar Fatakwal ta cigaba da sauraron shari’ar matashin nan Yunusa Dahiru da aka fi sani da Yunusa Yellow akan laifin safara da cin zarafin wata matashiya mai suna Ese Oruru.
A zaman na kotun na yau alkalin da ke saurar karar ya dage shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Maris.
A cikin watan Mayun shekarar 2020 ne wata babbar kotu a jihar Bayelsa ta yanke wa Yunusa Yellow daurin zaman gidan kaso na shekara 26 bisa samun shi da laifin safara da cin zarafin Ese Oruru.
Idan za a iya tunawa dai a shekarar 2015 ne dai mahaifan Ese Oruru suka yi zargin Yunusa Yellow da yin ‘garkuwa’ da yarsu, ya kuma kai ta jihar Kano inda ya tilasta mata aurensa har ma aka samu juna biyu.
Wannan batun dai ya jawo ka-ce-na-ce tsakanin ƴan kudu da arewacin Najeriya, musamman bayan da ta bayyana cewa Ese Oruru ta musulunta.
Barista Abdul Muhammad Rafindadi SAN da sauran tawagar wasu fitattun Lauyoyi ne su ke bin kadin shari’ar ta Yunusa Yellow.
