Connect with us

Featured

Kes ɗin Haneefa a Kotu: Shigowar ƴan siyasa cikin lamarin zai dagula al’amura

Idan DSS suka yi bincike, suka bi sawu, sannan suka yi nasarar kama mai laifi, sun gama aikinsu. Akan kes din Haneefa, an kai musu kuka, sun karba, kuma sun yi aikinsu. Sannan Allah ya basu dacewa.

Da suka tabbatar sun cika aikinsu, sun mika wa hukumar ‘yan sanda wanda suke zargi. Wanda suke zargi shi ne AbdulMalik Mohammed Tanko, shi ne ya saka matarsa da abokinsa da budurwarsa.

‘Yan sanda su ne za su yi dogon bincike da ilimi da lura, su tattara kwararan shaidu, su nemi shawarar masana na bangarorin aikinsu, su shirya takardar tuhuma First Information Report wato FIR. Idan sun shirya FIR za su kaiwa Babban magatakarda na jiha wato Chief Registrar ko mataimakansa ko sakataren JSC Judicial Service Council ya bada umarnin kotun da za ta yi shari’ar. Amma a irin wannan tuhuma ta mugun laifi Capital Offence, kwamishinan shari’a kuma antoni-janar huruminsa ne.

Da zarar an gama samun wannan umarni, ‘yan sanda za su dauko masu laifi daga inda ake tsare da su, sai a gurfanar da su gaban kuliya. A ranar farko dan sandan kotu zai karanta wannan tuhuma da harshen da wanda ake kara yake fahimta sarai. Za a karanta musu laifin da ake zargin sun aikata, da dokar da suka karya da tanadin hukuncin wanda ya yi wannan laifi. Za a yi musu bayani gwari-gwari. Idan an gama karatu, alkali zai tambaye su, sun saurara sosai, sun fahimta radau, shin sun aikata wannan laifi da ake zarginsu ko basu aikata ba? Har aka kaisu gidan ajiya a gidan gyaran hali ba a karanta musu wannan tuhuma ba.

A irin wannan tuhuma mai kara dole ya zama yana da lauya, suma da ake tuhuma dole su samu lauya da zai kare su. Idan ma ba su da shi akwai Legal Aid Council wadda hukuma ce ta gwamnatin tarayya, za su basu lauya. Sai a ci gaba da shari’a. Ba sha yanzu, magani yanzu bane.

A jiya Litinin da aka je kotu, kwamishinan ‘yan sanda da kansa ya halarta. Shi ma kwamishinan shari’a Barrister M.A Lawan da kansa ya halarta. Amma ba a baiwa wadanda ake tuhuma damar su amsa laifinsu ko su musanta ba. An jinkirta wannan bigiren sai nan da mako guda wato biyu ga watan Fabrairu na 2022. Dalilin jinkirin shi ne, kotun da aka kai su ta Alkali Muhammed Jibrin, Court 12 Gidan Murtala, bata da karfin sauraron irin wannan tuhuma sai dai ta sama da ita. Dole sai ‘yan sanda da ma’aikatar shari’a sun kimtsa sosai, don zuwa kotun gaba wato High Court akan wannan batu.

Akwai kotuna uku bayan High Court, akwai Court of Appeal, kotun daukaka kara, sannan akwai Supreme Court, kotun koli . Sai an bi duk matakai sannan za a iya yanke hukunci. In an yanke hukunci ma, sai an gabatar wa da gwamna Dr Abdullahi Ganduje in yana kan mulki, sannan ya saka hannu ya amince, ya bada izini. Wadannan matakai suna daukar lokaci mai yawa, saboda rashin kayan aiki da lalacewar kasa da son zuciya da siyasa.

Sai an yi da gaske Haneefa da iyayenta da mu al’ummar Najeriya zamu samu adalci. Ina tsoron cewa, shigowar masu siyasa cikin wannan sabgar, in ba a yi taka-tsantsan ba, zai iya dagula al’amura. Kada wannan lamarin ya zama riya da neman bajinta da kuam amfani da shi don biyan wata bukata. Haneefa tata ce ta fi bayyana a sarari kuma ta saka alhini mai daga hankali ga duniya. Amma an jima ana kashe yara kanana da mata da maza, a sace su, an dade ana kashe bil adama a kudu da arewa a kasar nan. An dade matsafa suna warkajaminsu. An dade ‘yan fashin daji da masu fashi da makami da ‘yan ta’adda suna kisan gilla da fyade da keta alfarma.

Tun da kisan gillar da aka yi wa Haneefa ya tada mana jijiyar wuya, mun harzuka, mun damu kada mu bari ya sha ruwa. Kada mu saka siyasa da zafin kai da rashin nutsuwa a ciki. Mu bi diddigi har sai mun samu adalci.

Bello Muhammad Sharada ya rubuto daga Kano

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet