Labarai
Ƴan bindiga a Katsina sun yi awon gaba da sama da mutane 50
Ƴan bindiga a jihar Katsina sun sake sace akalla mutane 50 a kauyen Ruwan Godiya dake karamar hukumar Faskari bayan wani ƙazamin harin da suka kai garin.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Jaridar ‘Daily Trust’ cewar ƴan bindiga sama da 60 bisa babura suka je garin inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
Mutumin ya ce ƴan bindigar sun kwashe sama da awa 2 suna cin karensu babu babbaka, inda suka kwashe dukiyoyin jama’a ciki har da kayan abinci da tufafi kafin su kora jama’a.
Jihar Katsina, wadda take jihar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito na ci gaba da fuskantar munanan hare hare daga ‘yan bindiga, wadanda ke halaka jama’a ba tare da kaukautawa ba.
Ko a ƙarshen makon da ya gabata sai da ‘yan bindigar suka kashe mutane 11 a karamar hukumar Ilela.
