Labarai
Rundunar Ƴan Sanda Ta Cafke Jami’in kASTLEA Bisa Zargin Dukan Direba Har Lahira A Kaduna
Rundunar ‘yan sanda ta kama wani jami’in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kaduna (KASTLEA) da ake zargi da lakada wa wani direban mota dukan tsiya har lahira a hanyar Ali Akilu, a cikin babban birnin Ungwan Sarki.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammad Jalige, ya ce kwamishinan ‘yan sandan, Mudassiru Abdullahi, ya bayar da umarnin kama shi ba tare da bata lokaci ba.
A cewar wadanda lamarin ya faru a gaban idanunsu, lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yamma, inda ya kai ga yin kaca-kaca a unguwar Ungwan Sarki da ke jihar.
An tattaro cewa an kashe direban ne bayan wata hatsaniya da jami’in kula da ababen hawa.
Wani ganau ya ce direban ya mutu ne sakamakon rauni a kai, inda ya kara da cewa an bugi marigayin da sanda a lokacin da suke takaddama.
ASP Jalige da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce kwamishinan ‘yan sandan ya bayar da umarnin kama jami’in kula da ababen hawa da ke da alhakin faruwar lamarin.
Jalige ya ce, “An samu hatsaniya tsakanin jami’an KASTLEA da wasu direbobi. Sun yi masa duka aka garzaya da shi asibiti inda ya rasu. Don haka direbobin suka yanke shawarar tare babbar hanyar domin nuna adawarsu amma mun hana su.
Maidaukar hoton ‘yan sandan ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike a kan lamarin da nufin gano musabbabin faruwar lamarin.
