Labarai
Tinubu Ba Zai Zame Min Barazana Ba, Cewar Dan Takarar Shugaban Ƙasa Orji Kalu
Wani dan takarar shugaban kasa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya ce tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ba zai kawo masa cikas ba a yunkurinsa na zama shugaban kasa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin Today Politics inda ya bayyana shirinsa ga kasar idan aka zabe shi ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Da aka tambaye shi ko yana kallon tsohon gwamnan a matsayin barazana, Kalu ya amsa da cewa, “A’a! kuma ni ba barazana bane ga burinsa. A lokacin da za mu hadu a dandalin Eagles, za a warware wannan batu.
“Ku sani, siyasa ba ta kudi ce kawai ba; game da al’ummar da za ku wakilta ne… mutanen arewa maso yamma, mutanen arewa maso gabas, mutanen arewa ta tsakiya, mutanen kudu maso gabas, mutanen kudu maso yamma, mutanen kudu maso kudu, kuma muna da jama’a. Zan iya motsa mutane kuma mutane suna tare da ni.”
Kalu da Tinubu dai jiga-jigan jam’iyyar (APC) ne mai mulki kuma sun yi gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007.
A watan Nuwamban da ya gabata, Tinubu ya ziyarci Kalu a gidansa da ke Abuja inda dukkansu suka yi wata ganawa a bayan fage, a dai dai lokacin da ake rade-radin cewa tsohon na sa ido a kan mafi girman mukami a kasar.
Bayan wata biyu da kammala ganawar, tsohon gwamnan na Legas ya kawo karshen wannan jita-jita bayan da ya ce ya sanar da shugaba Buhari aniyarsa ta ya gaje shi.
Ko da yake Kalu ya yarda cewa ba shi da wani shiri na zama shugaban kasa a lokacin da Tinubu ya ziyarce shi, ya bayyana cewa wasu yanayi ne suka sa shi sake tunani.
“Na gaya wa Tinubu cewa ba zan tsaya takara ba, gaskiya kenan,” in ji shi. “Lalle ne daga kudu maso gabas, kudu maso yamma, arewa maso yamma, arewa ta tsakiya, da arewa maso gabas ne ya sa na yanke shawarar shiga takarar. Na yi gwamna tare da shi (Tinubu), babu wani abu mai wahala wajen kalubalantar kowa.
“Dukkanmu za mu hadu ne a dandalin Eagle Square, kuma za mu shirya shi a can. Babu wahala. Ni kadai ne dan kasuwan siyasa da aka fara saninsa a matsayin hamshakin attajiri, kuma ban tabbata cewa akwai wani abu da wadannan mutane za su iya yi ba, ta fuskar kudi, da ba zan iya ba. Ba na jin za su iya magana da kowa a Najeriya ko a duniya da ba zan iya magana da shi ba.”
Akan abin da shugaba Buhari ke cewa game da matakin da ya dauka, Kalu ya kara da cewa, “Ban taba tattaunawa da shugaban kasa cewa ina son zama shugaban kasa ba.
“A karo na karshe da na gana da shugaba Buhari, na iya tattauna batutuwan da suka shafi kasa – ta’addanci, ‘yan fashi da makami, da yadda za a daidaita kasarmu, da sauran manyan batutuwan da suka shafi majalisar dokokin kasar kamar dokar zabe.”
