Labarai
Atiku Ya Ziyarci Jihar Benue, Ya Bada Kyautar Miliyan 50 Ga Ƴan Gudun Hijira
Atiku Abubakar ya ziyarci Jihar Benue, ya bada kyautar Naira miliyan 50 ga ‘yan gudun Hijra.
Daga: AbdulRasheeth Shehu
Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya kai ziyara jihar Benue, inda ya bada kyautar Naira miliyan 50 domin tallafawa yan gudun Hijra dake jihar.
A jawabin sa yayin da ya ziyarci gwamnati jihar Samuel Ortom, Atiku ya yi kira da a samar da karin tallafi ga yan gudun Hijra.
Tsohon mataimakin shugaban kasar har ila yau, ya kuma yi tsokaci kan yadda ya jagoranci bayar da gudummawa wajen yakar cutar Covid 19, abinda ya sanya wasu da yawa suka sami karfin gwiwar tallafawa.
Yayin da ya yi kira da a zauna lafiya tsakanin fulani da sauran kabilun dake jihar da kasa baki daya, ya yi gargadi kan danganta wata kabila da ayyukan laifi.
Ya kuma yabawa gwamnatin Gwamna Samuel Ortom, bisa kokarin sa na gina zaman lafiya a jihar, indai ya yi kira ga shugabanni su rungumi yan dukkan yan Najeriya ba tare da banbanci tsakanin su ba don siyasa ko addini ko kuma kabilanci Atiku Abubakar ya fadawa gwamnan cewar tun zuwan sa na karshe jihar a shekara ta 2019, ko da yaushe ya na son ganin yan gudun Hijrar.
”Bana dora wani laifi kan wani saboda kabilanci ko addini. A matsayin mu na shugabanni, kamata ya yi mu yi kokarin hada kan Jama’a, domin su fahimci junan su”
”A shekara ta 2019 ne nazo kuma na ziyarci wannan sansani na yan gudun Hijra, kuma tun sannan ban dawo ba, saboda haka ina sanar da bada gudummawata na Naira miliyan 50 domin kula da su.
Rahotoni sun ce kimanin mutane miliyan daya da rabi rikicin makiyaya da manoma ya raba da muhallin su a jihar, inda wasu da yawa sun rasa rayukan su.
