Connect with us

Labarai

Duk wacce aka yi lalata da ita kafin a saka ta a fim ta faɗa zamu ɗauki mataki – Nafisa Abdullahi

Tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta yi kira ga jarumai mata a masana’antar ta Kanywood da aka yi lalata dan za a sakata a cikin shirin fim ta fito ta bayyana dan su nema mata hakkinta.

Nafisa Abdullahi ta yi wannan kiran ne a wani rubutu da ta yi a shafinta na Facebook a yau Asabar.

“A kowanne profession akwai matsaloli daban-daban da mutane ke fuskanta, akwai masu cuta, akwai kuma wanda ake cutarwa”

“Zantuttukan da Naziru Ahmad yayi, zargi ne mai karfi (Serious Allegations) ne da ba’a ɗaukan su da sanyi ko a ina ne, a ciki har da ‘Sexual Assault’, wanda shi ne dalilin da ya sa na saka kaina a cikin abinda bai shafe ni ba”.

“Amma Kuma idan akayi la’akari da abinda ya faɗa ya shafe ni tunda mace ce ni”.

Jaruma Nafisa ta ƙara da cewa “Idan abinda yake faɗa gaskiya ne kuma yana da hujjoji da kuma shaidu, ina cikin mutanen da suke so su san su waye masu yin hakan! Tunda ya faɗawa duniya cewa ga abinda ake yi, to ƙarshen adalci ga wanda aka zalunta shi ne mu san su waye kuma mu ɗauki mataki akan su, dan a cikin dokokin (Laws) ɗin mu na ƙasar nan da kuma film industry ɗin, babu inda aka ce haka”.

A ƙarshe jarumar ta rufe kalaman na ta yin kiran da babbar murya akan duk wacce ta san haka ta faru da ita to fito sanar da duniya domin ɗaukar matakin da zai zama darasi ga masu wannan mummunar ɗabi’ar.

“Daga ƙarshe kuma duk macen da ta san an taɓa ce ma ta bayar da kan ta dan a sakata a cikin shirin to ta fito ta faɗa domin rashin bayyanawar ba zai magance matsalar ba balle har a kai ga samun gyara”.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet