Labarai
Kanywood: Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya za ta amarce
Fitacciyar Jarumar a masana’antar Kannywood Aisha Aliyu wadda aka fi sani da “Aisha Tsamiya” za ta yi aure.
Labarin ya bayyana ne a wani katin ɗaurin aure da shafin “Kannywood Celebrities” ya wallafa a Facebook da kuma Instagram.
Katin wanda ya fara yawo a kafafen sada zumunta ya nuna za a ɗaura auren jarumar a ranar Juma’a wato jibi kenan 25/2/2022 a Masallacin Sheikh Zarban, da ke Unguwar Ƴan Kaba Kwanan Ƴan Wanki kusa da gidan Tanko Yakasai bayan Sallar Juma’a.
Haka kuma Katin ya bayyana sunan wanda zai auri Jarumar da Alhaji Buba Abubakar.
Jarumar dai ta jima ba ta fita fitowa a sabin shirin fina-finai ko da a irin na “series” mai dogon zangon nan da ake yayi yanzu kuma bata sanar da ficewa ba daga masana’antar. Ta maida hankali kan kasuwancinta na sayar da kayan kwalliya da gyara jiki.
Sai dai har kawo haɗa wannan rahoton babu wani ƙarin bayani akan wannan batu daga jarumar.
