Labarai
Buhari ya baiwa kasar Afghanistan kyautar dala miliyan ɗaya
Ƙungiyar Haɗin kan Musulmi, OIC, ta yabawa Gwamnatin Taraiya bisa gagarumar kyautar da ta baiwa Gidauniyar Tallafin Jinƙai ta ƙasar Afghanistan.
Sakatare-Janar na OIC ɗin, Hissein Brahim Taha ne ya yi yabon a wata sanarwa da shelkwatar ƙungiyar ta fitar a yau Alhamis.
Sanarwar ta ce tallafin ya zo a daidai lokaci domin kungiyar ta samu damar ƙara ayyukan jin ƙai da a ke yi a Afghanistan.
Sanarwar ta ƙara da cewa Tallafin kuɗin zai taimaka a tallafa wa miliyoyin mutane maza da mata da ƙananan yara a Afghanistan.
A cikin watan Disambar shekarar 2021 ne ƙungiyar OIC ta kaddamar da Gidauniyar tallafin domin magance wahalar da al’umma su ke sha a Afghanistan a wani babban taro da ta haɗa.
Haka zalika Nijeriya ita ma mamba ce ta OIC din kuma na ɗaya da ga cikin ƙasashen da suka sanar da tallafin.
