Connect with us

Labarai

NNPP ko PDP?: Rabi’u Kwankwaso ya raba ƙafa a siyasar Najeriya

Wani rahoto da sashen Hausa na BBC ya rawaito ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar PDP mai hamayya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce zai fice daga jam’iyyar kafin karshen wannan watan nan na Maris.

Kwankwaso ya ce tuni shirye-shirye sun yi nisa a shirinsa na komawa jam’iyyar NNPP watau New Nigeria Peoples Party.

Sai dai kuma wani abu mai kama raba ƙafa a siyasa da gwamnan ya yi shi ne yadda shugabancin jam’iyyar PDP Kwankwasiyya a matakin jiha ƙarƙashin Shehu Wada Sagagi da kuma kananan hukumomi 44 da ke jihar Kano sun bayyana cewa suna nan a cikin jam’iyyar PDP daram.

Sanarwar wacce kakakin jam’iyyar Bashir Aminu Sanata ya fitar a safiyar yau Alhamis ta yi kira ga al’umma da su daina yaɗa labaran cewa shugabannin jam’iyyar ta PDP Kwankwasiyya sun koma jam’iyyar NNPP.

A watan jiya ne Kwankwaso ya jagoranci wani gagarumin taro na wasu manyan siyasar kasar karkashin wata kungiya mai suna The National Movement TNM.

A baya dai, Sanata Kwankwaso ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda jam’iyyar PDP take kokarin mayar da shi dan bora duk da gudunmawar da yake bayarwa a cikin jam’iyyar.

An dade ana kai ruwa rana tsakani tsohon gwamnan na Kano da bangaren tsohon ministan harkokin waje, Aminu Wali, wanda ake ganin ficewar ta Kwankwaso na da nasaba da rashin jituwar da ke tsakaninsu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet