Labarai
Kwalliya na biyan kuɗin sabulu a aikin da muke yi a ƙasar Ukraine – Putin
Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce yaƙinda ya ƙaddamar a Ukraine na tafiya yadda aka tsara.
Yana magana ne yayin wani jawabi da ya gabatar a ranar Larabar nan.
Ya nanata cewa suna yaƙi ne da dakarun ƙasar ba wai fararen hulla ba, waɗanda tuni gwamnatinsa ta ba wa damar ficewa daga wuraren da ake yaƙi.
Ya ƙara da cewa babban abun da suka sanya a gaba shine na ganin sun gurgunta tsaron Ukraine, da kuma kawar da barazanar da take kasar ke yi wa Rasha.
