Featured
Siyasar Kano: Wannene Ba Wanne ba ne? Jerin ƴan siyasar da ke burin gadon Ganduje
Kamar yadda ake yi wa kallon siyasar Kano sai ɗan Kano kuma ‘Kano ta dabo tumbin Giwa, ko da me ka zo an fika,’ hakan ya sa ake ganin zaɓen gwamna a shekarar 2023 a Kano zai fi zafi fiye da sauran jihohin Najeriya.
A lokacin da hadarin siyasa ya fara kaɗawa manyan ƴan siyasa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya su ka fara ƙulle – ƙulle da shige da fice irin siyasa domin ganin haƙarsu ta cimma ruwa wajen gadar kujerar gwamnan Kano daga hannun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kakar zaɓen shekarar 2023.
Shafin jaridar 21st CENTURY CHRONICLE ya yi nazari tare da sharhi akan jerin mutanen da su ka nuna sha’awarsu wajen gadon wannan kujera ta Gwamnan jihar Kano, inda kuma Kakaki Hausa su ka fassara sharhin.
1. Sanata Barau Ibrahim Jibrin
Sanata Barau Ibrahim Jibrin wanda aka fi sani da Maliya a fagen siyasar Kano shi ne Sanata mai wakiltar Arewacin Kano a zauren majalisar dattawan Najeriya.
Barau Jibrin wanda wannan shi ne karonsa na biyu a zauren majalisar dattawan Najeriya, ya kasance shi ne wanda ya ke kusa da samun tikitin takarar gwamnan Kano a tutar jam’iyyar APC kuma ake ganin zai iya kaiwa ga nasarar lashe babban zaɓen shekarar 2023.
Sai dai ya haɗu da cikas a wannan buri na sa a cikin jam’iyyar APC sakamakon raba gari da su ka yi da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Duk da haka masu sharhi akan siyasar Kano na kallon Sanata Barau wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne kuma shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawan Najeriya, a matsayin wani ɗan siyasa da ke da damar darewa kujerar gwamnan Kano, la’akari da yadda ya ke da goyon bayan al’ummar Arewacin Kano, da kuma yadda ya ke da kyauta a tsakankanin rukunin al’umma.
Sai dai wani cikas da Sanata Barau ɗin ya gamu da shi a burinsa shi ne jayayyar da ya ke yi da shugabancin Abdullahi Abbas Sanusi, wanda kuma shi ne wanda gwamnati ta aminta da shi yanzu.
Amma a wani yunƙurin na samun mafita da Sanata Barau Jibrin ɗin da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC G7 ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau, na da wani shiri na musamman wanda su ke kira da ‘Plan B’ da za su yi amfani da shi wajen cimma buƙatarsu ta siyasa.
2. General Ibrahim Sani
Manjo Janar Ibrahim Sani mai ritaya fitaccen mai taimakon al’umma ne a jihar Kano da kuma burin ganin matasa sun cigaba a harkokin rayuwa.
Bayan ya kammala aikin soja a rundunar sojin Najeriya, Janar Ibrahim Sani ya sadaukar da lokacinsa da dukiyarsa ne wajen ayyukan taimakon al’umma ta ƙarƙashin gidauniyar sa ta Gaskiya Ibrahim Sani wato Hasiya Ibrahim Sani Foundation (HISANEF).
A ƙarƙashin gidauniyar sa ta HISANEF, Janar Sani ya samarwa da al’umma na’urar taransfoma da samar da dakin gwaje-gwajen kimiyya a makarantun Sakandare da samar da ɗakunan karatun dalibai da gina cibiyoyin na’ura mai ƙwaƙwalwa da rijiyoyin Burtsatse a makarantun Sakandare da ke jihar Kano.
Haka kuma Manjo Janar Ibrahim Sani ya yi fice wajen gyarawa da gina magudanan ruwa a cikin birnin Kano, da baiwa mata masu juna biyu tallafin kayan da za su yi amfani da shi a lokacin haihuwa da kuma baiwa jami’an rundunar Hisbah horo akan na’ura mai ƙwaƙwalwa da kuma samar musu da kayan aiki na zamani a ƙoƙarin da su ke yi na yaƙi da mummunar ɗabi’ar nan ta shaye – shaye a tsakankanin matasa.
Wata majiya da ke kusa da tsohon Janar din ta bayyana cewa tuni abokai da makusantansa su ka fara tuntuɓarsa akan ya fito ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan Kano a zaɓen shekarar 2023.
Majiyar ta ce Janar Ibrahim Sani na da kyakyawar dangantaka tsakanisa da masu neman wannan kujera a jihar Kano.
Sai dai wani babban ƙalubale da ke gaban Janar Ibrahim Sani shi ne Mafi yawan al’ummar jihar Kano ba su san shi ba musamman a yankunan karkara da kuma ƴan siyasa na ƙasa.
3. Dakta Nasiru Yusuf Gawuna
Dakta Nasiru Yusuf Gawuna wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar Kano, wanda ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa, kuma kwamishinan ayyukan gona a yanzu haka yana daga cikin waɗanda su ke da burin neman kujerar gwamnan Kano a zaɓen shekarar 2023.
Dakta Nasiru Gawuna ya zama mataimakin Ganduje biyo bayan sauka da Farfesa Hafiz Abubakar ya yi bisa raɗin kan sa.
Haka kuma ana kallon rawar da Gwauna ya taka a dawowar Gwamnatin su a shekarar 2019 za ta ba shi dama wajen kaiwa ga nasarar gadon Ganduje a shekarar 2023.
Sai dai kuma wani abu da ake gani babbar nakasa ce da za ta zama cikas ga burin na Gawuna shi ne baya cikin waɗanda su ke da goyon bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a wannan ɓangare.
4. Murtala Sule Garo
Murtala Sule Garo, fitaccen ɗan siyasa ne a cikin jam’iyyar APC da ma jihar Kano.
Murtala Sule Garo na daga cikin ƴan siyasar da ake zancensu a da’irar siyasar Kano, kuma ya ke yaƙin sunkuru wajen ganin haƙansa ya cimma ruwa na shiga fadar gwamnatin Kano a matsayin Gwamna a shekarar 2023.
Haka kuma ana kallon Murtala Garo a matsayin ɗan siyasar da ke da goyon bayan shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano guda 44 da kuma mai ɗakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje.
Matashin ɗan siyasar ana kallon yana daga cikin kwamishina masu matuƙar tasiri wanda ake ganin zai yi amfani da ikonsa a tsakankanin shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano wajen cimma muradinsa.
Sai dai wani abu da ake ganin babban cikas ne ga Murtala Sule Garo ɗin shi ne yadda yan boko da masu rajin cigaban jihar Kano ke sukar kudirin Murtala ɗin bisa dalilan rashin cancanta da kuma dacewa wajen jan ragamar jihar Kanon.
Hakazalika wani ƙarin cikas ɗin ga Murtala Sule Garo shi ne yadda ya rasa goyon bayan ma’aikatan jihar Kano, bisa zargin da su ke yi masa da hannun wajen yanke musu albashi.
5. Kabiru Alhassan Rurum
Ɗan Majalisar wakilai mai wakilatar ƙananan hukumomin Rano da Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, yana daga cikin manyan ƴan siyasa da su ka fito daga yankin Kudancin Jihar Kano.
Tarihin siyasar Kabiru ya nuna cewa ya faro da yin Kansila a jihar Lagos, inda daga nan ya zama ɗan majalisar dokokin jihar Kano, daga bisani kuma ya zama Kakakin majalisar dokokin Kano.
Haka kuma a lokacin yana shugabantar majalisar dokokin jihar Kano, majalisar ta amince da tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga Sarautar Kano.
Ana kallon Kabiru Alhassan wanda shi ne Turakin Rano, ɗan siyasa ne da ke da goyon bayan ƴan siyasar Kudancin Kano da su ke ikirarin lokaci ya yi da mulkin jihar Kano zai koma Kudancin Kano.
Haka kuma ana kallon biyayyar da Kabiru Rurum ya ke yiwa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje za ta iya zama silar da za ta sa ya samu tikitin takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC. Sai dai kuma wasu masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar ba sa tare da Kabiru Rurum ɗin wanda hakan babban naƙasu ne ga burin na sa.
6. Barrister Inuwa Waya
A kwanan nan ne Barrister Inuwa Waya ya ajiye aiki a Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC, kuma tuni ya bayyana aniyarsa ta yin takarar kujerar gwamnan Kano.
Barrister Waya bai yi suna ba a farfajiyar siyasar jihar Kano, amma ana ganin cewa zai iya amfani da sanayya da ƙarfin tattalin arziki wajen samun tikitin takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar APC.
7. Senator Kabiru Ibrahim Gaya
Kabiru Ibrahim Gaya tsohon Gwamnan jihar Kano ne a lokacin tsohon Shugaban Mulkin Soja Ibrahim Babangida, daga 1992 zuwa 1993.
Sai dai masana siyasa a Kano na ganin cewa Kabiru Gaya ba da gaske yake ba a takarar tasa domin kuwa ya yi nisa da jama’a.
An yi amannar cewa a baya Kabiru Gaya ya yi amfani da takarar gwamna don ya ci gaba da zama a Majalisar Dattijai, kuma ana ganin a yanzu ma zai ƙara yin haka ne.
Wasu na ganin cewa lokaci yayi da dattijiya kamata ya je ya huta haka.
8. Abdulsalam Abdulkarim Zaura
Abdulsalam Abdulkarim Zaura, da aka fi sani da AA Zaura, ba sabon yankan rake ba ne a siyasar Kano saboda ya yi takarar gwamna a baya a jam’iyyar GPN.
Sai dai ya koma APC da nufin gadar buzun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a 2023.
A.A Zaura yakan yi yawo a ayarin motoci na alfarma, abin da yasa ake ganin kamar an ba shi tabbacin samun tikitin takarar.
Zaura yana da ƙwazo sosai wajen ɗaukar nauyin tafiyar da jam’iyyar APC a Kano.
Hamshaƙin ɗan kasuwa ne kuma abokin jagoran APC na ƙasa ne, Bola Ahmed Tinubu.
9. Muhuyi Magaji Rimin Gado
Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, tsohon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, shi ma wani ɗan takara ne da yake son ɗarewa kujerar Gwamnan Kano.
Muhuyi ya kasance daga cikin masu faɗa a ji a gwamnatin Ganduje kafin su ɓaɓe.
Bayan Muhuyi ya ɓaɓe da Ganduje ne sai aka ga fastocinsa sun cika gari a matsayin ɗan takarar gwamna.
Masana siyasa na ganin cewa komawarsa PDP alama ce dake nuna cewa da gaske yake yi a takarar tasa.
10. Engineer Mu’azu Magaji
Engineer Mu’azu Magaji (Ɗan Darauniya) shi ma wani jijjige ne a siyasar Kano. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tsige shi daga muƙamin Kwamishinan Ayyuka na Musamman bayan ya yi wani rubutu a shafinsa na Facebook game da mutuwar Abba Kyari.
11. Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf shi ne ya yi takarar gwamnan jihar Kano a PDP a shekarar 2019. Kuma har yanzu yana da farin jini a da’irar siyasar jihar.
Ko da ya ke dai har yanzu bai nuna sha’awarsa ta sake yin takara ba, masu sharhin siyasa na ganin cewa a koda yaushe Abba Gida Gida ɗan siyasa ne abin nema.
12. Ibrahim Ali Amin Little
Ibrahim Little shi ma ɗaya ne daga cikin ƴan takarar gwamnan Kano. Tuni dai Little ya sayi fom ɗin takarar gwamna a jam’iyyar PDP.
Malam Ibrahim Shekarau ne ya kayar da Little a zaɓen fidda na ANPP a 2023.
Little ya yi takarar gwamna a 2023 amma bai yi nasara ba. Ana ganin sa a matsayin gogaggen ɗan siyasa.
