Connect with us

Labarai

Tashin Bam ya jikkata mutum biyu a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da afkuwar wata fashewa, inda bam ɗin da ya tashi a Ƙaramar Hukumar Igabi ya raunata mutum biyu ranar Asabar.

Wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron cikin gida ta ce lamarin ya faru ne a Hayin Danmani lokacin da bam ɗin ya tarwatse a jikin wani babur mallakar wani mai suna Mohammed Hassan da ke sana’ar cire kuɗi a na’urar POS.

Rahoton ma’aikatar tsaron ya ce bayan mutumin ya tashi daga aiki ne kuma ya nufi babur ɗinsa don ya tafi gida, yana buga babur ɗin sai bam ɗin ya tashi da shi.

Ta ƙara da cewa fashewar ta ji wa Mohammed mummunan rauni da kuma wani mai wucewa da har yanzu ba a kai ga tantance ko wane ne ba. Kazalika, ta lalata rufin wani gini da ke kusa.

Tuni ‘yan sandan kwance bam suka isa wurin kuma sun yi nasarar kwance wani abin fashewar a jikin babur ɗin na Mohammed, a cewarta.

Yanzu haka waɗanda lamarin ya ritsa da su suna jinya a asibiti.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet