Labarai
2023: Atiku, Saraki, Tambuwal da Bala Mohammed sun sa labule
Masu neman shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP da su ka haɗa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Sanata Abubakar Bukola Saraki da Gwamna Bala na jihar Bauchi da kuma takwaransa Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto sun yi wata tattaunawa ta musamman a jiya Litinin.
Tun da farko tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki da Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, da na Bauchi Bala Mohammed da kuma Alhaji Mohammed Hayatuddeen, suka ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a kan batun yin sulhu.
Haka kuma zawarawan kujerar shugabancin Najeriya din sun bayyana cewa suna tattaunawa ne domin maslaha wajen fitar da mutum ɗaya daga cikinsu domin samun tikitin jam’iyyar PDP a babban zaɓen shekarar 2023.
