Connect with us

Featured

Nauyinmu har yanzu a wuyan Buhari ya ke – Bello Sharaɗa

Ɗazu da rana shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya yi zaman tsaro da manyan masu ba shi shawara a harkar. Sun bashi bahasin abin da ya faru a Kaduna jiya da daddare. Kafin ya gana da su Sufeto janar na Yan sanda da hafsan sojin kasa ya ziyarci inda wannan musiba ta faru.

Bayan an kammala zama da tattaunawa, shugaban kasa ya yi ta’aziyya da jaje kuma kamar yadda aka saba ya bada umarnin a cafko miyagun daji, kuma a kara tsaro da matakai.

Naga gwamna el Rufai ya ziyarci majinyata, kuma mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi takakkiya don ganewa idonsa.

ABIN DA YA KAMATA MU SANI

Miyagun daji a jihohin Kaduna da Neja da Zamfara da Katsina da Kebbi da Sakkwato mutane ne ba aljanu ba. Basu da wani suddabaru na musamman da suka fi karfin dabarun dan adam da shedancin mutum.

Miyagun daji tsageru ne, suna cin abinci, suna jin yunwa, suna jin harbi, suna rashin lafiya, suna mutuwa, suna fargaba, suna jin dadi kuma suna son rayuwa, basa son mutuwa. Suna da imani ragagge, sun kekashe zuciyoyinsu, kuma suna tarar aradu da ka.

Ya kamata mu sani, Miyagun daji ba sojoji bane kuma ba Yan sanda bane. Bindigogi suka mallaka shi ya sa ake tsoronsu.

Basu kai ‘yan sanda da soja kayan yaki da fada ba. Basu da kwarewa irinta jami’an tsaro. Basu da kayan aiki na fasaha irin na hukuma. Akan haramci suke zaune a jeji. Ta barauniyar hanya suke samun makamai. A kara zube suke rayuwa a jeji irin dabbobi, Al Mulku liman Qahara, wato mai karfi sai Allah ya isa. Jungle life.

Me yasa wadannan miyagun daji, ‘yan tsiraru suka gagari Najeriya.? Suka hana sakat a Kaduna da kauyukanta. Suka addabi Katsina da manyan biranenta? Suka cinye Zamfara da Sakkwato da Kebbi,? Suke yin yadda suke so a Neja?

Saboda kananan sojoji da ‘yan sanda da za su tunkare su a filin daga, can a jeji, ba su shirya mutuwa ba. Saboda manyan soji da ‘yan sanda da alhakin bada umarnin yake wuyansu, sun koma azzalumai, ‘yan rashawa, barayin zaune. Ko kadan ko kusa basa kula da walfayar kanana. Masu shiga soja da dan sanda, a yau, suna shiga ne don samun kudi ba domin kare kasa da kishinta ba.

Miyagun daji basa kera makamai, suna sayowa a kasuwar bayan fage. Suna sumogal dinsu. Jami’an tsaro sun lalace da ‘yan korensu, sune suke karbar na goro, mugu ya wuce da miyagun makamai.

A TAKAICE BA za a daina ganin tasku ba a harkar tsaro sai an yi gyara a aikin Yan sanda da soja. Sannan a gyara harkar shari’a.

Bello Muhammad Sharada ya rubuto daga Kano

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet