Connect with us

Labarai

Har yanzu ban kai ga yanke hukuncin ficewa daga jam’iyyar APC ba – Shekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Ibrahim Shekarau ya ce bai kai ga yanke shawara kan ficewa daga jam’iyyar APC ba.

An dai fara rade-radin cewa Sanatan da wasu manyan ’yan siyasa a Jihar sun kammala shirye-shiryen ficewa daga APC zuwa jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.

Hakan na zuwa ne bayan harsashen da ake yi cewa ba lallai ne Shekarau ya sake samun takarar ba a APC sakamakon rikicin Shugabancin da tsagin su ya tafka da na Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

To sai dai a hirar shi da jaridar Daily Trust ta wayar salula, mai magana da yawun tsohon Gwamna Shekarau, Dokta Sule Ya’u Sule, ya ce, ba su kai ga yanke shawarar ficewar ba tukunna.

A cewar sa, “Gaskiya ba wai an koma ba ne, akwai wasu abubuwa da muke ta tattaunawa a kai.

“Yanzu haka akwai taron da muke yi, amma gaskiya ba a dauki wata matsaya ba tukunna.

“Dole sai bayan wadannan tarukan da tattaunawar za a yanke hukunci, amma yanzu dai muna cikin jam’iyyar APC,” inji Dokta Sule.

Sauran wadanda ake rade-radin ficewar tasu daga APC sun hada da tsohon Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Sulaiman Kawu Sumaila, da tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar Rano/Kibiya/Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum.

Ko a makon da ya wuce dai mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano su tara sun sauya sheka da jam’iyyar PDP zuwa NNPP, wacce ke karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet