Connect with us

Labarai

Kaf jami’yyar APC babu wanda ya fi ni ƙwarewa na zama shugaban kasa a APC – Tinubu

Jagoran Jam’iyyar APC na ƙasa Bola Ahmed Tinubu yace kowa na iya bayyana sha’awar sa ta tsayawa takarar shugabancin kasar amma kuma ba kowa ke iya zama shugaban kasa ba.

Yayin da yake jawabi ga wakilan da zasu tsayar da ‘dan takarar shugaban kasar Jam’iyyar APC a Jihar Katsina, Tinubu yace shi yafi kowa kwarewa da cancanta tsakanin masu neman takarar shugabancin Najeriya daga Jam’iyyar sama da 20 da suka biya naira miliyan 100 domin fafatawa da shi.

Tinubu yace yana da kwarewar da ta dace na shugabanci yadda zai cirewa Najeriya kitse a wuta wajen fitar da ita daga mummunar yanayin da ta samu kanta musamman wadanda suka shafi tattalin arziki da tsaro.

Tsohon gwamnan na Jihar Lagos yace ya dace wakilan da zasu gudanar da zaben fidad gwanin da suyi la‘akari da tarihin ‘dan takara da kwarewar sa da horan da ya samu da kuma irin rawar da ya taka kafin fahimtar cewar ko zai iya sauya kasar daga halin talauci zuwa hanyar ci gaba.

Tinubu yace ya sha kan daukacin masu bukatar Jam’iyyar APC ta tsayar da su takara saboda haka shi yafi kowa dacewa a bashi amanar zama ‘dan takarar Jam’iyyar a zaben shekara mai zuwa.

Jagoran APC ya kuma bayyana bacin ransa dangane da ci gaba da yajin aikin malaman jami’oi, inda yayi alkawarin magance matsalar idan ya zama shugaban kasa.

Tinubu yace abin takaici ne yadda dalibai masu karatun shekaru 4 a jami’a kan kwashe shekaru 6 zuwa 10, saboda haka yace zasu zuba isassun kudade da kuma jarin da ya dace wajen ganin an baiwa matasan Najeriya ilimin da suke bukata.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet