Labarai
Jigawa: Ƴan sanda za su fara cafke masu yin lodi da yawa da masu tuƙin ganganci
Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa, ta umarci Jami’anta da su fara cafkewa tare ɗaukar matakan da suka dace akan dukkan direbobin da suke yin lodin da ya wuce ƙima da masu yin tuƙin ganganci.
Kwamishinan ƴan sandan Jihar Aliyu Sale Tafida, ne ya bada umarnin yayin ganawarsa da manema labarai da yammacin jiya Laraba a Dutse babban birnin jihar.
Kwamishinan ya ce, “Mun bada umarnin ne la’akari da cewa, kare rayuka da dukiyoyin al’umma su ne babban aikin rundunar ƴan sanda”.
Haka kuma ya ƙara da cewa, “Ba za mu bari wasu mutane su riƙa yin wasa da rayukan al’umma ta hanyar yin lodin da ya wuce kima ko kuma gudun wuce sa’a da tuƙin ganganci ba”.
