Labarai
Za a sake zaman sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU yau Alhamis
Manyan jami’an gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Ibrahim Gambari da Ministan Kwadago Chris Ngige, za su koma teburin sake tattaunawa da ƙungiyar malaman Jami’o’i ASUU.
Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labaran ma’aikatar Kwadago ta tarayya Olajide Oshundun ya fitar.
Sanarwar ta ce, za a gudanar da taron ne tare da mambobin sauran ƙungiyoyin kwadago har ma da wasu ƙungiyoyin Sa kai.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Farfesa Agboola Gambari, ne zai jagoranci zaman, kuma ana fatan samun maslaha tsakanin ɓangarorin biyu.
