Labarai
Gwamna El-Rufai ya haramta yin zanga-zangar da ke da alaƙa da addini
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya sanar da haramta yin duk wata zanga-zangar da ke da alaƙa da addini musamman wadda ke da alaƙa da kalama ɓatancin da ɗaliban nan Deborah ta yi kan Annabi Muhammadu SAW a Sokoto.
Hakan na cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin cikin gida da harkokin tsaron jihar ta fitar da yammacin yau Asabar mai ɗauke da sa hannun kwamashinan ma’aikatar Samuel Aruwan.
A cewar sanarwar gwamnatin ta ɗauki matakin ne bisa yuƙurin wasu mutane na yunƙurin shirya zanga-zanga kan lamarin.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna El-Rufai, ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar sun daƙile duk wata zanga-zangar addini a jihar.
