Labarai
Yadda maharan jirgin Abuja zuwa Kaduna suka sako wata mai ciki
Bayan ta shafe kwanaki 48, ƴan ta’addar da suka kai harin bam a kan jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna sun sako wata mata mai ɗauke da juna biyu.
An dai nuno matar da aka saki ɗin a cikin wani faifan Bidiyo tana sanye da baƙar abaya da abun rufe fuska inda aka yi ta yaɗa hoton a kafafen sada zumunta.
Wasu rahotonni sun nuna cewa ƴan ta’addan sun saki matar ne bisa tausaya mata da suka yi.
Jaridar Solacebase ta ruwaito, a wani hoton bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an nuno matar inda ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta tattauna da ƴan ta’addar don ganin an sako sauran mutanen da ke tsare wajen masu garkuwar.
A cewar matar, kiran nata ya zama wajibi saboda halin rashin tabbas da mutanen ke ciki a maɓoyar ƴan bindigar.
Haka kuma, ta ƙara da cewa ƴan ta’addar sun kula da su, inda ta ƙara da cewa suna ba su abinci sosai.
Ta kuma ce ‘yan ta’addan suna ba su magunguna.
Yayin harin wanda ɓata garin suka kai a watan Maris, sun kashe mutane tara tare da yin garkuwa da fasinjoji kusan 70 waɗanda har yanzu ake neman maɓoyarsu.
