Labarai
Sarkin Kano ya ziyarci Ofishin jakadancin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa don yin ta’aziyya
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kai ziyarci ta’aziyya a ofishin jakadancin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ke birnin tarayya Abuja bisa rasuwar shugaban ƙasar Sheikh Khalifa Bin Zayed Al Nahyan.
Sarkin ya kai ziyarar ne a Juma’ar nan jim kaɗan bayan ya dawo Najeriya daga ziyarar da ya kai kasar Senegal.
Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero, ya samu tarba ne daga Jakadan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a Najeriya Dakta Fahad Al Taffaq,
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, a jawabin ta’aziyyar tasa, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce, ƙasashen yankin Gulf da na yankin Gabas ta Tsakiya har ma da sauran ƙasashen, sun yi rashin babban jagora wanda ya ba da gudummawa ta fuskar sadaukar da kansa wajen wanzar da zaman lafiya da harkokin tsaron ƙasa da ƙasa.
Haka kuma ya ce, “Haƙiƙa Masarautar Kano ta yi alhinin wannan wannan babban rashi da zai yi wuyar cike gibinsa”.
Haka kuma ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da sanya wa marigayi Sheikh Al-Nahyan ladan ayyukan alherin da ya bari.
A nasa ɓangaren Jakadan na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a Najeriya, ya gode wa sarkin bisa ziyarar tare da yi masa addu’o’in fatan alheri.
