Uncategorized
Ƴan sanda sun yi harbe-harbe don tarwatsa masu zanga-zangar kama Rochas Okorocha
Rahotonni daga birnin tarayya Abuja, sun bayyana cewa jami’an ƴan sanda sun yi harbe-harbe cikin iska a gidan tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha domin tarwatsa masu zanga-zangar adawa da kama shi.
BBC ta ruwaito cewa, masu zanga-zangar mutane ne da ke cin gajiyar tsohon gwamnan don haka suke yunƙurin hana cafke shi.
Haka kuma ta ruwaito cewa tun da fari jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC da jami’an ƴan sanda yayin yunƙurin cafke Rochas, sun kuma umarci manema labarai da su bar gidan nasa.
A yau ne jami’an EFCC, suka yi dirar mikiya a gidan Rochas Okorocha, domin kama shi bisa ƙin amsa gayyatar da suka yi masa.
