Labarai
Yadda jami’an EFCC suka mamaye gidan Rochas Okorocha domin cafke shi
Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC suka mamaye gidan tsohon gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha, domin kama shi.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, da safiyar Talatar nan ne aka gano wani faifan bidiyo da ya nuna jami’an hukumar sun mamaye gidan nasa wanda ya ke a unguwar Maitama a birnin tarayya Abuja.
Haka zalika ta ƙara da cewa yayin dirar mikiya da jami’an sun mamaye harabar gidan.
Jami’an na EFCC sun kafe kai da fata cewa ko dai Rochas Okorocha ya miƙa kansa gare su ko kuma ya amsa wata tsohuwar gayyata da hukumar ta yi masa.
