Connect with us

Siyasa

Sha’aban Sharada ya buƙaci jam’iyyar APC ta rushe zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna na Kano

Mai neman takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar APC Sha’aban Ibrahim Sharada, ya buƙaci uwar jam’iyyar APC da ta rushe zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar da aka gudanar a jihar Kano.

Sha’aban ya buƙaci hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook bayan da ya yi watsi da sakamakon zaɓen da aka fitar da ya nuna cewa matakin gwamna Nasir Yusuf Gawuna ne ya samu nasara.

Ɗan majalisar ya bayyana zaɓen fidda gwanin a matsayin wani aiki wanda aka tafka kura-kurai da sayen ƙuri’a da kuma tsoratarwa don haka ya buƙaci da a soke zaɓen.

A daren jiya Alhamis ne aka gudanar da zaɓen fitar da gwani na gwamnan a filin wasa na Sani Abacha.

“Na tsallake rijiya da baya bisa wani yunkurin kisa, a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar mu na gwamna da ya gudana a Kano, Mintuna kaɗan da fara aikin, jami’an tsaro suka gargaɗe ni da cewa kada na zo wurin da za a yi zaɓen, a lokaci guda kuma na samu sakon kar ta kwana daga shugaban kwamitin zaben fidda gwani a gaban Sanata Tijjani Kaura yana kira na. su kasance a wurin da za a fara zaben”.

“Abin da ya ba ni mamaki, an nemi jami’an tsaron da aka turo daga Abuja don bani kariya da su tafi wurin da za a gudanar da zaɓen,” in ji Sharada a cikin sanarwar da ya fitar.

Haka kuma, Ya ƙara da cewa an kai wa da yawa daga cikin magoya bayansa hari kuma a cikin haka ne wasu daga cikinsu suka rasa rayukansu.

“Yayin da ake ci gaba da zaɓen, akwai wasu tsare-tsare na amfani da ƴan daba da kuma kawo ƙarshen rayuwata a lokacin da nake fitowa daga wurin taron, Daga baya ma na samu wani rahoton sirri na cewa waɗannan ƴan barandan sun riga sun kai hari har sun kashe da kuma raunata dimbin magoya bayana wanda hakan ya sa na yi gaggawar ficewa daga wurin taron na wuce asibiti inda ake kula da lafiyarsu, Don haka a gare ni ran mutum ɗaya ya fi daraja a kan siyasa da kuma zama Gwamna,” inji shi.

“Don haka, ina kira ga jami’an tsaro da babbar jam’iyyar mu da su yi bincike da gaske tare da hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika tare da gaggauta soke zaɓen fidda gwanin da aka tafka kura-kurai, sayen kuri’u da kuma tsoratarwa, hakan ba ya nuna manufar babbar jam’iyyarmu da dimokuradiyya ta gaskiya, Yayin da yake tabbatar wa dandazon magoya bayanmu cewa za mu ci gaba da fafutukar kwatowa da dawo da martabar jiharmu, wannan yunkurin ba zai sanya ni karaya ba na dakatar da ayyukan alheri da muke yi.” Inji Sha’aban.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet