Connect with us

Labarai

Zargin almundahana: Majalisar dokokin Kaduna ta dakatar da wasu shugabannin ƙananan hukumomi

Mjalisar dokokin jihar Kaduna, ta ɗauki matakin dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Chikun Malam Salisu Musa, da na ƙaramar hukumar Giwa Abubakar Lawal, bisa zargin su da almundahanar wasu maƙudan kuɗi.

Majalisar ƙarƙashin jagorancin shugabanta Alhaji Yusuf Zailani ta ɗauki matakin ne yayin zamanta na Talatar makonnan sakamakon ƙudurin da wakilin mazaɓar Zaria Kewaye, Alhaji Ahmed Chokali ya gabatar.

Mamban ya gabatar da buƙatar cewa ya kamata majalisar ta gudanar da bincike kan lamarin.

“Na miƙe ne domin gabatar da ƙudirin gudanar da bincike ƙarkashin sashe na 128 na kundin tsarin mulkin Najeriya domin a binciki al’amuran ƙananan hukumomi biyu na jihar nan,” inji shi.

Haka kuma ya buƙaci majalisar da ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin ne domin samun damar gudanar da cikakken bincike.

Majalisar ta kuma umurci shugabannin ƙananan hukumomin da su miƙa al’amuran mulki ga mataimakan su, tare da umurtar kwamitinta mai kula da harkokin ƙananan hukumomi kan ya gudanar da bincike tare da gabatar mata da rahoton bincikensa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet