Siyasa
Jam’iyyar APC ta yi watsi da mutane 10 masu neman takarar shugaban ƙasa
Kwamatin tantance masu son shiga takarar fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, yaƙi tantance ƴan takara 10.
Shugaban kwamatin John Oyegun ne ya bayyana hakan yau Juma’a.
Ya ce mutane goma sha uku ne suka tsallake tantancewar da kwamatin ya yi musu.
Haka kuma ya ƙara da cewa Yace ƴan takarar da suka tsallake ne kaɗai za su fafata a zaɓen fitar da gwani wanda jam’iyyar za ta gudanar ranar 6 da kuma 8 ga wannan wata da muke ciki na Yuni.
