Featured
Kano: Mutane da dama sun fita daga hayyacinsu sakamakon shaƙar wani sinadari
Rahotonni daga yankin rukunnin masana’antu na uku da ke Sharada a jihar Kano na cewa, wasu mazauna unguwar Mundaɗu da dama sun fita daga hayyacinsu sakamakon shaƙar hayaƙin wani sinadari.
Da yammacin yau Juma’a ne gidan rediyon Freedom ya fara kwarmata rahoton faruwa lamarin yana mai cewa iftila’in ya faru ne sakamakon fashewar wata tukunyar sinadari ta masana’antu wadda ke ɗauke da guba.
Haka kuma ta ruwaito cewa lamarin ya samo asali ne daga wani wurin masu yin sana’ar gwangwan da ke unguwar inda mai unguwar yankin Malam Magaji Abdullahi ya tabbatar da faruwar al’amarin yana mai cewa an garzaya asibiti da mutane da dama.
