Featured
Harin jirgin ƙasa: Ɗangin mutanen da aka sace sun musanta sako su
Wasu daga ciki dangin fasinjojin da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su na jiragin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, sun musanta labarin da ake yadawa a shafukan sada zumunta da ke cewa ƴan bindiga sun saki ƴan uwansu.
Hakan dai na cikin wata sanarwa da shugabanin ƙungiyar ƴan uwan fasinjojin Drlakta Abdulfatai Jimoh da kuma Dakta Ba’aba Muhammad suka fitar.
Ta cikin sanarwar sun ce, batun sakin ƴan uwan nasu labarin shifcin gizo ne kawai.
Sun ƙara da cewa, kawai an yi ta yaɗawa ne a kafafen sada zumunta wanda kuma ba haka batun yake ba.
