Addini
Maniyyata ƴan Najeriya 1,354 ne suka sauka a Madina
Ya zuwa yammacin Asabar ɗin an, kimanin maniyyata ƴan asalin Najeriya mutum dubu ɗaya da ɗari uku da hamsin da huɗu ne suka isa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
Kuma an sauke su ne a birnin Madina kamar yadda hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta bayyana.
BBC ta ruwaito cewa maniyyatan da ke birnin na Madina akwai maza ɗari da saba’in da ɗaya da kuma mata ɗari da saba’in da shida.
Haka kuma ta ƙara da cewa adadin maniyyatan ya ƙaru bayan da jirgin FLYNAS ya sauka da fasinjoji ɗari uku da arba’in da bakwai da kuma jami’an gwamnati ashirin da uku, bayan da Jirgin ya tashi daga filin jirgin sama na Abuja a yau.
