Connect with us

Labarai

Ƴan bindiga sun sace ƴan kasuwa a hanyar Zamfara zuwa Sokoto

Wasu ƴan bindiga, sun sace ƴan kasuwa kusan mutum arba’in a kan hanyarsu ta zuwa jihar Zamfara daga Sokoto.

BBC ta ruwaito cewa mafi yawa daga cikin waɗanda ƴan bindigar suka yi garkuwa da su masu gudanar da sana’ar sayar da wayoyin hannu ne a kasuwar Bebeji Plaza da ke Jihar Zamfara.

Haka kuma ta ƙara da cewa, fiye da mutane sittin ƴan bindigar suka tare a hanyar, sai dai fiye da ashirin daga ciki sun arce.

Haka kuma kafar BBC ta ce, a zantawarta da Shugaban kasuwar ta Bebeji Plaza, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa, an yi garkuwa da su ne jiya Asabar a hanyar su ta komawa daga ɗaurin aure da suka je Sokoto.

Haka kuma ya ce, ƴan kasuwar na tafiya ne a mota ƙirar Coaster mai ɗaukar mutane arba’in da kuma wata mota ƙirar bus mai ɗaukar mutane 18.

Ita ma rundunar ƴan sandan jiha Zamfara, ta bakin mai magana da yawunta ƴan SP Muhammad Shehu ta tabbatar da faruwar lamarin.

SP Muhammad Shehu, ya ƙara da cewa, tuni jami’an rundunar suka duƙufa wajen gano maɓoyar ƴan bindigar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet