Labarai
Ƴan bindiga sun sake sakin wasu daga ciki fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna
Ƴan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin ƙasa Kaduna zuwa Abuja a ranar 28 ga watan Maris & in da ya gabata, sun ƙara sakin wasu daga cikin fasinjojin jiya Asabar.
Jaridar Desert Herald ta ruwaito cewa sai dai mutane 11 ƴan bindigar suka saki saɓanin dukkan matan da ke tsare a hannunsu da suka yi wa gwamnati alƙawari.
Mawallafin jaridar Malam Tukur Mamu wanda ke a matsayin mai shiga tsakani domin samun daidaito gwamnatin tarayya da ƴan bindigar ya bayyana cewa mata shida kaɗai ƴan bindigar suka sako da kuma maza biyar.
