Labarai
Hajjin Bana: Hukumar NDLEA ta gargaɗi maniyyata kan miyagun ƙwayoyi
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta gargaɗi maniyyata aikin Hajjin bana kan safarar miyagun ƙwayoyi.
Jami’ar hukumar Habiba Zubairu, ce ta yi gargaɗin ga wasu maniyyata a birnin Illori na Jihar Kwara.
Haka kuma ta shaida wa maniyyatan cewa iya magungunan da likitoci suka ba da izinin sha ne za a iya tafiya da su, don kuwa mahukuntan ƙasar Saudiyya ba za su aminta da shiga da wasu su ba.
Haka kuma ta ja kunnen maniyyata da su guji karɓar kayan wani da sunan riƙo ko ajiya domin gujewa da-na-sani.
