Siyasa
Da ɗumi-ɗumi: Atiku ya zaɓi Ifeanyi Okowa a matsayin abokin yin takara
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen baɗi Alhaji Atiku Abubakar, ya zabi gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa, a matsayin mataikinsa idan ya samu nasara a zaɓen.
Tashar Talabijin ta Arise ta ruwaito cewa Atiku ya sanar da hakan ne da tsakar ranar yau Alhamis.
Haka kuma tashar ta bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasar a PDP ya bayyana zaɓar Okowa ne a shalkwatar jam’iyyar da ke birnin tarayya Abuja.
