Connect with us

Labarai

Kano: Ƴan sanda sun cafke kwararren ɗan damfara a Internet

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta ce, ta cafke wani matashi da ake zargin yana amfani da shafukan bogi na kafafen sada zumunta domin yaudara da damfarar mutane.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana rahoton kama matashin a shafinsa na Facebook.

SP Kiyawa ya ce, jami’an ƴan sanda sun kama matashin ne mai suna Musa Lurwanu mai shekaru 26 bayan da suka tattara wasu bayanan sirri tare da bin diddigin abubuwan da yake aikatawa.

Haka kuma ya ƙara da cewa rundunar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe ne a kan matashin ƙaurin sunan da matashin ya yi wajen amfani da sunayen maza da mata yana damfarar mutane tun a watan Afrilun da ya gabata.

Haka kuma Kiyawa ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya yi ƙaurin suna a kafafen sada zumunta na Facebook da Twitter da Whatsapp da sauran kafafen sada zumunta ta hanyar amfani da sunayen maza da mata inda yake yaudarar mutane ta hanyar wallafa hotuna.

Ya ƙara da cewa ƴan sanda sun karɓi ƙorafi daga wata matashiya Zahra Mansur mai shekara 20 wadda ta ce, abokanta da ƴan uwa na ta kiranta sakamakon wani na amfani da sunanta da hotonta da bidiyoyi wurin buɗe shafukan Facebook da kuma yaudarar jama’a.

Rundunar ƴan sandan ta jihar Kano ta kuma ce, ta cafke Musa Lurwanu, tare da samunsa da wayar hannu ƙirar Redmi Note 11 Pro ta kimanin Naira Dubu ɗari biyu da sauran wasu kayayyaki.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet