Tsaro
Kano: Ƴan sanda sun cafke wani matashi bisa zargin kashe ƙanin mahaifinsa
Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta ce ta cafke wani matashi bisa zarginsa da kashe kanin mahaifinsa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai da yammacin yau Alhamis.
Ya ce, ana zargin matashin Jibril Shua’ibu da hallaka marigayin Abdullahi Yusuf ta hanyar dukansa da taɓarya a garin Jodade da ke yankin ƙaramar hukumar Kunchi.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ƙara da cewa, rundunar za ta gurfanar da matashin a gaban kotu da zarar ta kammala bincike a kansana.
