Labarai
Amotekun Ta Kama Wasu Bisa Zarginsu Da Hannu A Kai Harin Coci A Jihar Ondo
Rundunar tsaro a jihar Ondo ta Amotekun ta kama wasu mutane da ake zargi da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa masu ibada a cocin St. Francis Catholic da ke Owo, a jihar ta Ondo.
Kwamandan rundunar, Adetunji Adeleye ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Akure, babban birnin jihar.
Adeleye, bai bayyana ainihin adadin wadanda ake zargin da aka kama ba, amma shugaban kungiyar ya yi fatan za a gurfanar da duk wanda ke da hannu a harin Owo.
Da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Ondo domin jin ta bakin mai magana da yawunta, SP Funmilayo Odunlami, ta ce rundunar ba ta da masaniyar haka.
Sai dai ana sa ran rundunar Amotekun za ta mika wadanda ake zargin ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su gaban kuliya.
Hakan dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a hukunta wadanda suka kai harin da ya bayyana a matsayin ‘matsorata’ da suka kai hari a wasu coci-coci a kasar.
“Game da matsorata, za a hukunta su kan laifukan da suka aikata. Za mu gurfanar da su gaban kotu. Ku tabbatar da cewa kwazon jami’an tsaro da na leken asiri na Najeriya,” inji Buhari a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar.
“A yanzu haka, ina kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su hadu mu yi addu’a-ko Kirista, Musulmi, ko wani babban addinanmu- mu rike wadanda abin ya shafa da iyalansu a cikin zukatanmu.
“Mu nunawa matsorata da ke neman raba kan mu ta hanyar addini cewa ba za a raba mu ba. Mu nuna musu cewa ’yan Najeriya za su ci gaba da daraja abin da muke bauta tare da mutunta bambance-bambancen juna. Mu nuna musu cewa matsorata, masu tsatsauran ra’ayi, ko ‘yan ta’adda ba za su taba cin zarafin ‘yan Najeriya ba.”
A cewar shugaba Buhari, ‘yancin addini da bambancin addini ne ke sa Najeriya ta zama babba.
