Connect with us

Uncategorized

Harin Ofishin ‘Yan Sanda Na Akure Ya Yi Sanadiyyar Rasa Ran Jami’i Guda

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da harin da aka kai dibishin din ta na Okuta Elerinla da ke Akure a karamar hukumar Akure ta Kudu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Funmilayo Odunlali, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin din nan a Akure, ta ce harin da aka kai ofishin ‘yan sanda ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin jami’anta.

“A ranar 25 ga watan Yuli, da misalin karfe 1:00 na safe, wasu ‘yan bindiga sun kai hari Okuta Elerinla Dibishin na Akure.

“’Yan sandan da suke cikin aiki a lokacin kuma suna raye suna aikinsu sun fatattake su a kan haka kuma barayin sun kasa samun damar shiga ofishin.

“Lokacin da lamarin ya faru, daya daga cikin masu kula da ofishin mu mai lamba AP.2075380 sufeto Boluwaji Temenu ya samu harbin bindiga, daga baya ya mutu a hanyarsa ta zuwa asibiti,” inji ta.

Odunlali ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Oyeyemi Oyediran, ya umarci hukumar binciken manyan laifuka ta jihar da ta binciki lamarin tare da tabbatar da kama wadanda suka aikata laifin.

A halin da ake ciki, CP Oyediran ya bukaci al’ummar jihar da su gudanar da aikinsu na ko da yaushe ba tare da fargaba ba, yana mai jaddada cewa nan ba da jimawa ba za a kama masu shirya harin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

(NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet