Kasuwanci
Yadda Najeriya Za Ta Biya Bashi A Cikin Kwanaki 90 – Sanata Ibrahim
Zababben sanata kuma hamshakin dan kasuwa Dr. Jimoh Ibrahim ya yin gabatar da wani jawabi ya bayyana yadda Nigeria za ta biya bashin da ake binta cikin kwanaki 90 kacal.
Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today, Ibrahim ya ce ya kamata hukumomi su tunkari bankunan EXIM guda biyar, su karbi lamunj wanda ya ninka bashin da ake bin kasar a yanzu.
“Zan iya ba ku dabarar da za ta sa ku iya biyan bashin a cikin kwanaki 90”
“Abun da kawai za ku yi shi ne ku kira bankunan EXIM guda biyar, ciki har da bankin EXIM na China” inji shi.
“Ku kabi lamuni sau biyar fiye da duk abun da ake bi a halin yanzu, ku aiwatar da kudaden tazarar da zai biya kansa, sannan ku biya wanda ake bi, sannan za ku samu ragi, ku yi shirin biyan kudin shekara 40 sannan ku samu karramawa na shekara 10 shi kenan kun fita daga bashin”.
A cikin shirin, dan kasuwar wanda dan asalin jihar Ondo ne ya kuma yi tsokaci kan kalubalen tsaro da Nijeria ke fuskanta musamman rikicin Boko Haran da ya addabi al’ummar kasar sama da shekaru goma.
Ya kuma bayyana Boko Haram a matsayin matsalar siyasa, inda ya nemi shugaban kaaa da ya mayar da sojoji Nigeria sansaninsu.
Ya kuma dora laifin gazawar da ake zargin an yi wajen yaki da ta’addanci a kan dabarun da hukumomi suke bi a yankin Arewa Maso Gabas.
