Labarai
APC Ta Soki Rusau Din Da Gwamnatin Kano Ta Ke Gudanarwa
Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta soki yadda ake rusa gine-ginen da gwamnatin jihar Kano ta jam’iyyar NNPP ke yi a jihar.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Alhaji Shehu Maigari ne ya yi Allah-wadai da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar ‘yan jarida ta NUJ da ke Kano a ranar Talata.
“Kano kasancewarta babban birni kuma cibiyar kasuwanci ta yankin Arewa da sauran kasashen yammacin Afirka, yanzu tana fuskantar babban bala’i daga gwamnatin NNPP.
“Wannan barna da rashin gaskiya da Gwamnatin jihar ta ke yi wa al’umma, yana kira ga duk masu kishin Kasa da su yi addu’a sosai, domin a yanzu jama’a na kirga asarar da suka yi ta biliyoyin Naira,” inji Maigari.
Ya ce rugujewar ta kawo koma baya inda har aka daina harkokin kasuwanci a fitattun kasuwannin Kantin Kwari da Kofar Wambai da sauran cibiyoyin kasuwanci a cikin birnin.
