Labarai
Katsina: An karrama ɗan sandan da ya mayar da kuɗin tsintuwa
Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta karrama wani jami’inta mai suna Nura Mande, bisa mayar da Dalar Amurka dubu takwas da ya tsinta ga mai su.
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Gambo Isah, ya fitar.
Ta cikin sanarwar Gambo Isah ya ce, kwamishinan ƴan sandan jihar Idris Dabban, ya miƙa wa jami’in nasu takardar yabo da kuma kuɗi Naira dubu talatin a jiya Juma’a.
Haka kuma ya ƙara da cewa Nura Mande yana aiki ne a sansanin jin dadin alhazai na jihar Katsina inda ya gano Dala dubu takwas na wata maniyyaciyar hajjin bana Hajiya Hadiza Usman.
“Yayin da yake gudanar da aikinsa a sansanin Hajji, PC Mande ya gano dala 800 a ƙasa sannan ya mayar wa Daraktan gudanarwa na hukumar, Alhaji Sada Salisu-Rumah.
“PC Mande ya bayyana cewa tsoron Allah ne ya sa ya mayar da kuɗin ga jami’in hukumar domin a mayar wa mai shi.
“Salisu-Rumah ya yaba wa ɗan sandan bisa kyawawan halayensa da kuma gaskiya,” ya kara da cewa.
A cewar Isah, kwamishinan ƴan sandan ya ji daɗin yadda Mande ya nuna gaskiya, ya kuma yi kira ga sauran ‘yan sanda da ke cikin rundunar da su yi koyi da shi.
Ya kuma ce, rundunar za ta ci gaba da yaba wa jami’anta wadanda suka nuna gaskiya da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
