Labarai
Sarkin Kano da tawagarsa sun dawo daga ƙasar Morocco
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero tare da ƴan tawagar sa, sun dawo daga ƙasar Morocco.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa sarkin da waɗanda suka yi masa rakiya sun dawo ne cikin daren jiya Litinin bayan bayan da suka shafe mako guda a wata ziyarar aiki da suka kai masarautar Morocco bisa gayyatar Sarki Mohammed na biyar
Haka kuma ta bayyana cewa, Sarkin ya gudanar da taruka da jami’an ƙasar ta Morocco da kuma ziyartar wasu manyan biranen kasar da wuraren tarihi waɗanda suka haɗa da Casablanca da Marrakech da Rabat da kuma Fes.
Haka kuma, Sarkin ya kuma ziyarci Cibiyar horas da limamai da masu wa’azi da ke Rabat inda ya gana da shugabannin Cibiyar tare da neman karin tallafin karatu domin taimaka wa matasa da sauran masu sha’awar ci gaba da karatu a fannin addinin Musulunci.
