Connect with us

Labarai

Shugaba Buhari ya tafi ƙasar Portugal

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya tafi ƙasar Portugal, domin amsa gayyatar sa da shugaban ƙasar Marcelo Rebelo de Sousa ya yi masa.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkar yaɗa labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a yau Talata.

Sanarwar ta ce, shugaba Buhari zai ziyarci majalisar ƙasar domin ganawa da kakakinta Dakta Augusto Santo Silva da Firayi Ministan Portugal Antonio Costa.

Haka kuma ta cikin sanarwar Malam Garba Shehu, ya ce yayin ziyarar, shugaba Buhari zai gana da ƙungiyar ƴan kasuwar Najeriya mazauna Portugal tare da yin wani taron da shugabannin kamfanoni da wasu ƴan kasuwa da ke da niyyar  zuba jari a Najeriya.

Haka kuma a cewar sanarwar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, zai halarci taron majalisar ɗinkin duniya watau United Nations Ocean Conference, wanda aka fara a birnin Lisbon daga jiya Litinin zuwa 1 ga watan gobe na Yuli.

Solacebase ta ruwaito cewa Shugaba Buhari zai kuma tattauna da ƴan Najeriya mazauna ƙasar  kan abubuwan da ke damunsu da kuma harkokin ci gaba a Najeriya, inda ake sa ran shugaban zai dawo Abuja a ranar Asabar mai zuwa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet