Labarai
Ƙasar Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan Dhul Hijjah
Ƙasar Saudiyya ta sanar da ganin jaririn watan Dhul Hijjah, watau watan Babbar Sallah.
Shafin da ke kula da Masallatai biyu masu daraja Haramain Sharifain ne ya bayyana ganin ganin watan a shafinsa Facebook.
Mahukuntan ƙasar sun bayyana ganin jaririn watan ne a yau Laraba.
Haka kuma sun ce, gobe Alhamis 30 ga watan Yuni shi ne ɗaya ga watan Dhul Hijjah.
Wannan sanarwa dai na nuni da cewa, Za a yi tsayuwar Arfa ranar Juma’a 8 ga watan gobe na Yuli, yayin da kuma. babbar sallar za ta kama ranar Asabar 9 ga Yuli.
