Tsaro
Hukumar NCoS ta tabbatar da kai hari gidan gyaran hali na Kuje
Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya NCoS, ta tabbatar da rahoton cewa ƴan bindiga sun kai hari gidan gyaran hali na Kuje, da ke birnin tarayya a Talatar makonnan.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Umar Abubakar ya fitar.
Sanarwar ta ce, “Wasu ƴan bindiga da ba a kai ga gano su ba sun kai hari gidan gyaran hali na Kuje, da ke yankin babban birnin tarayyar Najeriya.”
“jami’an hukumar tare da taimakon sauran jami’an tsaro sun mayar da martani kan maharan, kuma yanzu haka an mayar da doka da oda a gidan.” kamar yadda jaridar Solacebase ta ruwaito.
