Labarai
Harin jirgin ƙasa: An biya Miliyan 800 kafin sakin mutane 7
Rahotonni daga dangin mutane bakwai da ƴan bindiga suka saki a baya-bayannan, sun bayyana cewa, An biya Naira miliyan ɗari takwas ga ƴan ta’addan da ke tsare da mutanen gabanin sakin waɗanda aka sace su a jirgin ƙasa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Jaridar Solacebase, ta ruwaito cewa, a ranar Asabar din da ta gabata ne yan bindigar suka sako mutanen bakwai, sai dai a ranar Lahadi wasu cikin makusntan mutanen sun ce sai da suka biya kudin gabanin sakin nasu.
A ranar 28 ga watan Maris, din da ya gabata ne yan bindiga suka farmaki jirgin kasan tare da sace fasinjojin wanda kuma har kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
Sai dai wasu majiyoyin tsaro da masu bincike sun alakanta harin da kakkausar murya ga ragowar mayakan Boko Haram da ke aiki tare da ‘yan kungiyar Darul Salam, wata kungiyar da galibin matasan Fulani ne da aka kora daga jihohin Neja da Nasarawa a lokuta daban-daban.
Sai dai wasu na alakanta harin da kungiyar IS da ke yammacin Afirka watau ISWAP.
