Connect with us

Uncategorized

Wata Babbar Kotu Ta Bada Umarni Na Wucin Gadi Game da Ciyo Bashin Biliyan 10 Na Gwamnatin Kano

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Talata, ta yi watsi da umarnin wucin gadi da tun farko ta bayar na hana gwamnatin jihar Kano rancen Naira biliyan 10.

Dokta Yusuf Isyaka-Rabiu, babban darakta na gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu, ta Kano First Forum (KFF) ne ya shigar da karar yana neman a ba da umarnin hana gwamnatin jihar Kano ciyo bashin Naira biliyan 10.

Wadanda ake kara a karar sun hada da Gwamnan Kano, Babban Lauyan Jihar Kano, Kwamishinan Kudi na Kano da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Sauran sun hada da Bankin Access, Ma’aikatar Kudi ta tarayya, Ofishin Kula da Bashi da Hukumar Kula da Kudi.

Solacebase ta ruwaito cewa tun da farko kotu ta hana gwamnati ciyo bashin kudin siyo na’urar daukar hoto ta CCTV wato Closed-Circuit Television (CCTV) da kyamarori da don ci gaba da magance matsalar tsaro.

Mai shari’a Abdullahi Liman ya kori umarnin na wucin gadi da aka bayar a ranar 1 ga watan Yuli, bayan lauyan wadanda ake kara, Muhammad Dahuru, ya bukaci kotun da ta yi watsi da umarnin da ta bayar a baya a kan abokan huldarta.

Liman ya kori umarnin ne bisa la’akari da kuskuren da mai nema ya nuna da kuma ɓoye bayanan gaskiya.

Ya mayar da shari’ar zuwa kotun zuwa bayan hutu domin babbar kotun tarayya za ta fara hutun shekara a ranar Juma’a.

Za a sanar da ranar da cigaba ga bangarorin biyu.

Tun da farko, Lauyan wadanda ake kara, Mista Muhammad Dahuru, ya shigar da kara mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Yuli, inda ya bukaci kotun da ta yi watsi da umarnin da ta bayar a baya kan wadanda yake karewa.

“Sakamakon kalubalen tsaro da ya danganci ‘yan fashi da garkuwa da mutane a kasar, wanda ya kamata a yi taka tsantsan don kare rayuka da dukiyoyi.”

Lauyan mai kara, Mista Badamasi Suleiman, ya shigar da rubutacciyar adireshi guda biyar inda ya nuna adawa da bukatar da wanda ake kara ya shigar na neman a ba da umarnin wucin gadi da tun da farko ta bayar na hana gwamnatin jihar ciyo bashin Naira biliyan 10.

NAN ta ruwaito cewa KFF na kalubalantar gwamnan jihar Kano kan ciyo bashin naira biliyan 10 bisa zargin rashin bin ka’idoji da hada hadar rance ko ciyo bashi.

Masu neman aikin, a cikin rokonsu, sun kalubalanci gwamnatin jihar ba tare da bin dokar kafa ofishin kula da basussuka ba, 2003, Fiscal Responsibility Act, 2007 da Laws of Kano, 1968.

NAN ta kuma kara da cewa a ranar 15 ga watan Yuni ne majalisar dokokin jihar ta amince da bukatar Ganduje na ranto naira biliyan 10 daga bankin Access.

(NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet