Featured
Gwamnatin Ganduje ta hana hawa Adaidaita sahu bayan 10:00 na dare
Gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta haramta yin amfani da baburan Adaidata Sahu bayan ƙarfe 10:00 na dare.
Hakan na cikin sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar a yau Litinin.
Sanarwar ta ce, gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin magance matsalar tsaro da jihar ke fama da ita.
Malam Muhammad Garba ta cikin sanarwar ya kuma bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis ɗin makon nan.
Haka kuma sanarwar ta buƙaci masu tuƙa baburan na Adaidaita Sahu da su kasance masu bin dokar da gwamnatin ta sanya.
