Labarai
Hukumar INEC ta fara yiwa masu larurar Kuturta rijistar zaɓe
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta fara gudanar da aikin yi wa mutanen da ke ɗauke da larurar kuturta rajistar zaɓe ta din-din-din a Jihar Neja.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter a yau Asabar.
BBC ta ruwaito cewa hukumar ta fara yi wa masu larurar rijistar ne yau Asabar a sansanin su da ke ƙaramar hukumar Chanchaga.
Haka kuma ta bayyana cewa hukumar ta ɗauki matakin ne a yunƙurin da take yi na ganin an bai wa kowane ɗan Najeriya dama wajen kaɗa ƙuri’a a zaɓe baɗi da ke ƙaratowa.
