Labarai
Gwamnan Jihar kogi Ya Dakatar Da Basaraken Gargajiya
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayar da umarnin dakatar da Ohi na Eganyi kuma shugaban majalisar gargajiya ta Ajaokuta, HRH Alhaji Musa Isah Achuja da gaggawa.
A wata wasika da gwamnan ya aikewa kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Kogi, gwamnan ya kuma umarci da a tambayi shugaban karamar hukumar Ajaokuta, Honarabul Mustapha Aka’aba a kan sabawa doka kuma ya amsa cikin sa’o’i 24.
Umurnin da gwamnan ya bayar a kan mutanen da abin ya shafa na da nasaba da tabarbarewar tsaro a yankin da ya yi sanadin mutuwar wasu jami’an tsaro bisa kokarinsu na tabbatar da doka da oda.
Gwamnan ya yi kakkausar gargadi ga sauran sarakunan gargajiya a fadin jihar da ke da alaka ta wata hanya ko kuma wata alaka da masu aikata miyagun laifuka a yankunansu da su kau da kai, yana mai cewa gwamnatinsa za ta yi kakkausar suka ga duk wanda ke soyayya da masu aikata miyagun laifuka komai girman sa.
Hakazalika, Gwamna Bello ya kuma ba da umarnin hana duk wani yunkuri na shugabannin kananan hukumomi fita daga yankinsu da sauran tafiye-tafiye ba tare da bin ka’ida ba.
Gwamnan ya yi gargadin cewa babu wata alaka da masu aikata miyagun laifuka da za su hana shi daga babban nauyin da ke kansa na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da mazauna jihar.
Yan kwanton bauna
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a ranar Asabar din nan da yamma sun yi wa jami’an tsaro kwanton bauna a unguwar Jidda-Bassa da ke karamar hukumar Ajaokuta a jihar Kogi, inda suka kashe ‘yan sanda uku da ‘yan banga biya wato yan bijilanti.
An tattaro daga wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta cewa wasu mutane da ke zaune a unguwar Jidda-Bassa sun kai rahoto ga jami’in ‘yan sanda na shiyya cewa wasu mutanen da ba a san ko su waye ba sun kai hari gonakinsu, suna kwashe kayan amfanin gona.
Majiyar ta ci gaba da cewa baturan yan sanda yankin DPO ya tattaro wasu daga cikin mutanensa da ’yan banga zuwa wurin, amma kafin su isa gonar, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi musu kwanton bauna.
Majiyar ta ce yayin harin an kashe ‘yan sanda uku da ‘yan banga biyar wato yan bijilanti.
Majiyar ta kara da cewa an ajiye gawarwakin wadanda aka kashe a dakin ajiye gawa na Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Kogi ta sha alwashin kamo wadanda ke da hannu a kisan.
Mai baiwa gwamnan jihar Kogi shawara kan harkokin tsaro Jerry Omodara ne ya bayyana haka yayin da yake tabbatar da faruwar harin a wata zantawa da ya yi da wakilin gidan talabijin na Channels ta wayar tarho a Lokoja.
Ya ce gwamnatin jihar za ta dauki matakan da suka dace domin kamo alhakin lamarin tare da nuna cewa duk wadanda ke da hannu a kashe-kashen ba shakka za a kama su.
Omodara ya kara da cewa gwamnatin jihar na yin iya bakin kokarinta wajen ganin an dakile masu aikata laifuka a jihar.
